Matakan Da Manoman Jihar Taraba Suka Dauka Kan 'Yan Ta'adda
Manage episode 452374800 series 3311743
Wata matsala da kasar nan ke cigaba da fuskanta itace matsalar karancin abinci sakamakon ‘yan ta’adda dake barnata amfanin noma, hana manoma yin noma, a wasu lokutan ma karbar kudaden haraji daga manoma a wasu yankunan kasar nan.
Hakan yasa alummomin Karamar hukumar Gassol da Balli dake jihar Taraba daukar wasu matakai don samawa kan su mafita daga ayyukan irin wadannan yan ta’adda.
Shirin Najeriya A Yau na wannan rana zai tattauna ne kan irin matakan da alummar wadannan yankuna suka dauka don gudanar da ayyukan noma.
704 odcinków